Jordan ta nemi ficewa daga takunkumin da aka saka wa Siriya
Kasar Jordan ta nemi Kungiyar Kasashen Larabawa data tsameta daga cikin masu kakarawa kasar Siriya takunkumin kararraya ta, saboda rashin bada hadin kai domin shawo kan rikicin kasar.
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yawun maaikatar Waje na kasar ta Jordan Mohammed Kayid, ya fadawa kamfanin Dillancin labaran Faransa, AFP, cewa suna goyon bayan kungiyar kasashen Larabawa amma kuma saboda takunkumin zai shafe ta bata ciki.
Taron da aka yi a Doha na kasar Qatar, ranar Asabar na kungiyar kasashen Larabawa ya lissafa wasu jami'an kasar Siriya 19, da aka malkaya masu takunkumin hana su zirga-zirga cikin kasashen Larabawan kuma dukiyarsu da suka jibge a kasashen sun yi bankwana dasu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu