Syria
Kungiyar kasashen Larabawa za ta tura masu saka ido Syria
Shugaban Kungiyar kasashen Larabawa Nabil al-Arabi dazun yake fadin cewa ayarin masu sa idanu kan irin wainar da ake toyawa a kasar Syria na kan hanyar su nan da kwanaki uku.
Wallafawa ranar:
Talla
Kungiyar Larabawa ce dai ta lallashi Hukumomin kasar Syria dasu amince da bukatar, domin a shiga kasar aga kuma aji zarge-zargen da ake tayi cewa Hukumomin kasar na ta kashe jama'a.
Ya fadi cewa ayarin masu sa idanun sun hada da jami'an tsaro, masu rajin kare hakkin dan Adam, masana sharia da manema labarai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu