Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Shugaban Korea ta arewa Kim Jong-Il ya mutu

Shugaban Kasar Korea ta Arewa, Kim Jong-Ill, ya rasu ranar Assabar yana da shekaru 69 a duniya. Wata sanarwa da aka bayar ta gidan talabijin na kasar, ya nuna cewa, shugaban ya rasu da misalin karfe 8:30 na safe agogon kasar, wato 11:30 ranar juma’a agogon GMT, sakamakon bugun zuciya.

Tsohon Shugaban kasar Kim Jong-il wanda ya mutu yana da shekaru 69
Tsohon Shugaban kasar Kim Jong-il wanda ya mutu yana da shekaru 69 REUTERS
Talla

Kamfanin dillancin labaran kasar, yace shugaban ya rasu ne a cikin jirgin kasa, yayin da ya ke ziyara a wajen babban birnin kasar, inda sanarwar ta bukaci yin mubaya’a ga Dan sa, Kim Jong-Un.

An dai haifi tsohon shugaban ne a shekarar 1942, inda ya shiga jami’a a shekarar 1960, kafn fara aiki a shekarar 1964.

Ya tsaya takarar zabe a shekarar 1982 inda aka zabe shi Dan Majalisa, kafin ya gaji mahaifinsa Kim Il-Sung a shekarar 1994.

An dade ana zarginsa da cin zarafin Bil Adama, da kuma kai hari Kasar Myammar, inda ya kashe sojin Korea ta kudu 17, da kuma harbo jirgin saman Korea ta kudu, mai dauke da mutane 115.

Shugaban ya kuma kaddamar da aikin samar da makamin nukiliya, abinda ya sa shi fito-na-fito da shugabanin kasashen duniya, kuma har rasuwar sa bai bada kai bori ya hau ba, duk da tattaunawar da aka dade ana yi.

A ranar 28 ga watan Disemba ne za’a yi Jana’izar shugaban.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.