Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Iran ta gargadi matuka jirgin ruwan Amurka

Sojan kasar Iran sun gargadi wani katon jirgin ruwan kasar Amurka na kwasan jiragen sama na yaki, da kada ya kuskura ya tsoma kafarsa yankin ruwan Iran, in kuma ba haka ba, komi ya same shi shi ya jiyo.Babban Hafsan Sojan Iran, Brig-Gen Ataollah Salehi ya fadi cewa basu da lokacin sake wani gargadi ga kasar Amurka. Janar Salehi yace su a wajen su gargadin daya ya wadatar.Gargadin na zuwa ne bayan kammala atasayen kwanaki 10 da Dakarun Ruwan kasar Iran suka yi a yankin nasu domin kara shiri kada a yi masu sakiyar da ba ruwa.  

Sojan Iran suna atisayen su, kwanakin baya
Sojan Iran suna atisayen su, kwanakin baya Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.