Isa ga babban shafi
Singapore

Za’a zabtare albashin shugabannin Singapore domin ci gaban kasa

Hukumomin Kasar Singapore, sun sanar da shirin zabtare albashin shugabanin kasar, da kashi daya bisa uku na abinda ake biyansu, saboda magance fushin jama’ar kasar, bayan zaben da aka yi a bara.

Fira Ministan kasar singapore  Lee Hsien Long
Fira Ministan kasar singapore Lee Hsien Long AFP
Talla

Rage albashin ya biyo bayan alkawarin da Fira Ministan kasar Lee Hsien Loong ya yi, na rage kashi 51 na albashin shugaban kasar, na jeka na-yi-ka, yayin da zai rage nashi kashi 36 na albashin da yake karba Dala Miliyan 1.69.

An bayyana albashin shugaban kasar Singapore matsayin albashi mafi tsoka tsakanin shugabannin kasashen duniya wanda ya linka albashin shugaban Amurka Barack Obama sau biyu wanda ke karbar kudi dala $400,000.

Tun samun ‘Yancin kasar ne daga Malaysia a Shekarar 1965, Jam’iyyar PAP ke shugabancin kasar kafin shekarar 2011 da aka yi rabon kuri’u tsakaninta da sauran Jam’iyyun adawa.

Sai dai duk da wannan zabtare albashin shugabannin, gwamnatin kasar tace zasu samu kudaden lada kimanin albashinsu na watanni uku idan har aka samu ci gaba a kasar tare da samar da aikin yi ga matasa.

An bayyana cewa Fira Ministan kasar Japan yana karbar albashin kudi Dala $513,000 duk shekara. Fira Ministan kasar Australia kuma tana karbar albashin kudi Dala $379,000 duk shekara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.