MDD ta ce mutane 7,500 sun hallaka cikin rikicin kasar Syria
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa, yanzu haka an kashe mutane 7,500 a ci gaba da tashin hankalin da ake a kasar Syria.Kasar Faransa ta bukaci Rasha da China da su goyi bayan kudirin kawo karshen zub da jinin, da kuma kai kayan agaji ga mabukata, yayin da kasashen biyu ke bayyana bacin ransu kan sukar da Amurka ke musu kan Syrian.
Wallafawa ranar:
Tuni kasar ta Amurka na rubuta wani sabon daftari dan mikawa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, domin barin kai kayan agaji zuwa Syria, inda dubban mutane ke bukata.
Wannan zai zama karo na uku da kasashen Yammacin Duniya ke gabatar da irin wannan kudiri, wanda Rasha da China ke hawa kujerar naki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu