Isa ga babban shafi
Syria-EU

Kasashen Turai zasu haramtawa matar Assad yawo

Wani Jami’in diflomasiya yace Ministocin kasashen Turai zasu amince da takunkumin hana yawo da rufe asusun ajiyar matar shugaban kasar Syria Bashar Assad da aka Haifa a Birtaniya.

REUTERS/Yves Herman
Talla

Kasashen sun ce Asma al Assad tana cikin manyan Jami’an gwamnatin Syria 12 hadi da shugaban kasa da zasu fuskanci Takunkumi.

An zargi gwamnatin Assad da kashe dubban masu zanga zangar adawa da gwamnatinsa.

Asma Assad mai shekaru 34 na haihuwa ta kwashe rayuwarta a birnin London, amma babu wani tasiri da matar ke takawa a gwamnatin mijinta a Syria.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.