Isa ga babban shafi
Iraqi

Taron kasashen Larabawa a Iraqi zai mayar da hankali akan Syria

A karon farko Shugabannin kasashen Larabawa zasu gudanar da babban taronsu a Bagadaza babban birnin kasar Iraqi, inda ake hasashen taron zai mayar da hankali game da yadda za’a kawo karshen rikicin kasar Syria.

Ministan harakokin wajen kasar Iraqi Hoshiyar Zebari a lokacin da yake fara gabatar da jawabi a taron kasashen Larabawa da ake gudanarwa a Bagadaza tare da Ahmed Bin Hilly na Tarayyar Larabawa
Ministan harakokin wajen kasar Iraqi Hoshiyar Zebari a lokacin da yake fara gabatar da jawabi a taron kasashen Larabawa da ake gudanarwa a Bagadaza tare da Ahmed Bin Hilly na Tarayyar Larabawa REUTERS/Saad Shalash
Talla

Daruruwan jami’an tsaro ne aka girke a Bagadaza tare da dakili layukan Salula da manyan hanyoyi da rufe filin saukar jirgi domin kaucewa hare hare.

Yanzu haka shugabannin kasashen Larabawa sun fara hallara taron tare da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon wanda zai sa bakin shi domin tattauna batutuwa da dama da suka hada da yadda za’a kawo karshen rikicin Larabawa da Isra’ila.

Taron zai kunshi shugabannin kasashen Larabawa 22 da suka hada da kasar Qatar da Saudiyya wadanda suka gabatar da kudirin tattauna kawo karshen rikicin Syria.

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane 9,000 ne aka kashe tun fara zanga-zangar kin jinin gwamnatin Bashar Assad na Syria.

An bayyana cewa dakarun kasar Iraqi 100,000 ne aka girke domin samar da tsaro a Bagadaza, kuma kasar Iraqi ta kashe kudade dala Miliyan 500 domin gyara masaukin baki da zauren gudanar da taron.

Sai dai duk da matakan tsaron da kasar Iraqi ke dauka a ranar Talata wani dan kunar bakin wake ya kashe mutane uku cikinsu har da Dan sanda a Bagadaza.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.