Isa ga babban shafi
Bangladesh

Zanga zanga ta barke a Bangladesh bayan salwantar madugun adawa

Dubban mutane ne suka fito domin gudanar da zanga-zanga a kasar Bangladesh bayan kwashe kwanaki shida ba tare da jin duriyar Madugun adawa Ilias Ali. ‘Yan Sanda sun ce an samu mutuwar mutum daya amma wasu 20 suka samu rauni.

Daruruwan magoya bayan Gwamnatin Bangladesh lokacin da suke neman tunkarar gangamin da 'Yan adawa suka hada domin adawa da gwamnatin kasar
Daruruwan magoya bayan Gwamnatin Bangladesh lokacin da suke neman tunkarar gangamin da 'Yan adawa suka hada domin adawa da gwamnatin kasar REUTERS/Andrew Biraj
Talla

‘Yan rajin kare hakkin Bil’adama a kasar, suna zargin Jami’an tsaro wajen cafke ‘Yan adawa a asirce tare da zarginsu da aikata laifin karya doka.

Ali shi ne babban dan siyasar Jam’iyyar BNP kuma babban mai adawa da gwamnatin kasar Bangladesh. Yanzu Ali shi ne babban dan siyasar da ya bata tun shekarar 2009 da Jam’iyyar Fira minista ta Sheikh Hasina Awami ta karbe mulki.

A Dhaka babban birnin kasar a yau Litinin an rufe makarantu da kasuwanni bayan shiga kwanaki biyu na zangar zangar salwantar Ilias Ali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.