Isa ga babban shafi
Yemen-Alka'ida

Sojan gwamnatin Yamen sun kusa kwace garin Zanjibar daga yan Alka'ida

 Dakarun sojan kasar Yamen sun bayyana daukar sabin dubaru a yakin da suke yi da dakarun kungiyar Alka’ida tun farkon watan mayun 2011 da ta gabata a garin Zinjibar dake yankin kudancin kasar ta Yamen.Majiyar ta bayyana cewa, yanzu haka sojojin kasar na ci gaba da nausawa a tsakkiyar garin , cikin , mummunan fada, a yankunan gudu da kuma gabashin garin na Zinjibar, majiyar ta kara da cewa, dakarun sojan gwamnatin sun kama muhimman gurare da suka hada da wata maikatar aika wasiku.A halin yanzu dai, an bayyana cewa, dakarun na Alka’ida sun fara gudu suna ficewa daga garin da ya kasance babban birnin yankin Abayane, da ke arewacin Aden. 

Exército iemenita se apresenta em Sanaa.
Exército iemenita se apresenta em Sanaa. REUTERS/Khaled Abdullah
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.