Saudi Arabiya
kasar Saudiya ta zartar da hukuncin kisa kan wani mutum
Yau da safe a kasar Saudiyya aka fille kan wani mutun saboda laifin kisan kai a garin Asir dake kudu maso gabashin kasar.Mutumin mai suna Zaher Bin Ali al-Shihri an same shi da hannu tsundum wajen dabawa abokin sa Moh ~Bin Hadi, wuka bayan wata yar gajeruwar gardama tsakanin su biyun.Mutane 21 kenan aka fille masu kai a kasar saboda laifukan da suka sabawa dokokin kasar mai bin tsarin dokar musulunci sau da kafa.
Wallafawa ranar: