Isa ga babban shafi
Syria

Akalla dakarun gwamnatin kasar Syriya 20 ne suka rasa rayukansu a yau litanin

A yau litanin wasu hare-hare sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama mafiya yawansu kuma dakarun tsaron kasar Syriya a garin Ibleb dake yankin arewa maso yammacin kasar, kwana guda bayan isar janar Robet Mood shugaban tawagar masu zura ido MDD kan yarjejeniyar tsagaita buda wuta, a kasar ta Syriya inda tashe tashen hankulla suka yi sanadiyar mutuwar mutane 70 a wannan mako.Sama da mutane 20 mafi yawansu mambobin rundunar tsaron kasar suka rasa rayukansu a cikin fashewa da ta wakana a garin na Iblem, kamar yadda kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar OSDH ta sanar. Wasu fashe-fashen guda 2 kuma sun wakana a cibiyar binciken jiragen sama da kuma hukumar bayanan soja na kasar suma sun yi sanadiyar mutuwar mutane.  

Le quartier de Bab Dreeb à Homs, le 12 avril 2012.
Le quartier de Bab Dreeb à Homs, le 12 avril 2012. Reuters/Shaam News Network/Handout
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.