Isa ga babban shafi
Isra'ila

Wasu Fursunonin Falastinawa 2 dake yajin kin cin abinci sun bayyana a gaban babbar kotun kasar Izra'ila

Wasu palastinawa 2 da kasar Izra’ila ke tsare da su, wadanda ke yajin kin cin abinci yau da kwanaki 65 da suka gabata, a yau alhamis sun bayyana a gaban madaukakiyar kotun kasar, wace ta sake duba bukatar da suka gabatar na neman a sake su, kamar yadda lauyan kungioyar kare hakkin dan adam ta palastinawa ya sanar a yau.Thaer Halahla dan shekaru 34 da Bilal Diab dan shekaru 27 wadanda aka zarga da zama yan kungiyar jahadin Islama ta palastinawa, sun shigar da karar a gaban kotun ne, kan ci gaba da tsaresu da ake yi ba tare da tuhuma ba. A jere a jere na farko an kama shi ne tun cikin watan yuni na 2010, a yayin da na 2 wanda aka kama a watan Ogusta na 2011 da suka gabata.karar da suka shigar a gaban kotun ta shafi fannoni guda 2 wadanda suka hada da ci gaba da tsaresu ba tare da tuhuma, sai kuma hujjarsu ta shiga yajin kin cin abinci, kamar yadda lauyansu Jamil Khatib ya sanar.Kotun dai ta bayyana cewa, dukkanin batutuwan da suka fada ya zama wajibi a duba su, domin Izara’ilar ta taka dokokin duniya na tsare fursunoni ba tare da shara’a ba, haka kuma ko wane fursuna na bukatar samun ingantaciyar rayuwa a inda ake tsare da shi.Yanzu haka dai kashi 1 bisa 3 na fursuninin Falastinawa dubu 4.700 da Izra’ilar ke tsare da su, sun tsunduma cikin yajin kin cin abinci sakamakon rashin kyawan yanayin da ake tsare da su a ciki, kamar yadda hukumar kula da gidajen yarin kasar ta Sanar. 

cinkoson wasu fursunoni a cikin kaso
cinkoson wasu fursunoni a cikin kaso Reuters/Nacho Doce
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.