Syria
Shugaban kungiyar yan adawar kasar Syriya ya aje mukaminsa
Jagoran Babbar kungiyar ‘yan adawa ta kasar Syria Burhan Ghallion ya bayyana ajiye mukaminsa yau, kafin a gabatar da wanda zai karbeshi, kwanaki biyu rak da zabensa.Wata sanarwa na cewa, zai ci gaba da kasancewa cikin majalisar rikon kungiyar tasu da aka kafa tun watan 10 na shekarar data gabata.Ajiye mukamin nasa na biyo bayan zarge-zarge ne da wasu kungiyoyin dake fafutukan kawar da Gwamnatin kasar ke yi, na kane-kane da uwar kungiyar ke yi gameda duk wata harka.
Wallafawa ranar: