Isa ga babban shafi
Syria

Assad ya kori Jekadun kasashen Turai 11 a Syria

Shugaban Kasar Syria, Bashar al Assad, ya kori Jakadun kasashe 11 na Yammacin duniya, a wani mataki na mayar da martani a kan yadda aka kori wasu Jakadun kasar a makon jiya.

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad todayszama
Talla

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Syria ke ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kaasshen duniya, dan kawo karshen zubar da jinin da ake samu a kasar, da bukatar shugaba Assad ya sauka daga karagar mulki.

Jekadun kasashen sun hada da Canada da Italia da Spain Belgium, Bulgaria da Jamus.

A ganawar shugabannin Rasha da China a Beijing, kasashen biyu sun ce zasu yi kokarin ganin cim ma bukatun Kofi Annan mai shiga tsakanin rikicin kasar.

Kasashen Biyu sun dade suna hawa kujerar na-ki a zauren Majalisar Dinkin Duniya akan lkalubalantar Gwamnatin Bashar Al Assad.

‘Yan rajin tabbatar da Demokradiya a kasar sun ce sama da mutane 13,500 ne suka mutu a Syria tun fara zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bashar al Assad.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.