Shugaban Korea ta Arewa ya kore rade radin cewa bashi da aure
An kawar da rade radin da ake yi na cewa shugaban kasar Korea ta Arewa, Kim Jong- Un, bashi da aure, bayan wani gidan talabijin kasar ya nuna shi da wata mata wacce aka bayyana a mtasayin matarsa a wani taro.Gidan talabijin din kasar ya nuna shugaba Jong-Un tare da wata mata a wani taron kammala gina wani wajen shakatawa a Pyongyang.
Wallafawa ranar:
An dade an yayata cewa Jong-Un bashi da aure amma ganinsa da aka yi da wannan mata wacce jama’a su ka ga an basu kyakyawan tarbo ya kore wannan rade radin.
Sai dai ba a san ko yaushe ne shugaban kasar ya auri wannan mata ba wacce ake kira Ri Sol- -Ju.
Gidan talabijin din ya kuma nuna shugaba Jong –Un ya na murmushi tare da matarsa a yayin da ya ke tattaki cikin wajen shakatawan tare da kusosihin jam’iyarsa da kuma manyan hafsoshin sojin da ‘yan diplomasiyar kasar.
An dai fara ganin shugaban da Sol-Ju wacce bata da tsawon gashi a wani taron shakatawa a ranar 5 ga watan Yulin wannan shekara.
An kuma kara ganin shi da ita a ranar 8 ga watan Yulin wannan shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu