Isa ga babban shafi
Japan

Al’ummar Japan suna bukin tuna bala’in Hiroshima

Dubban mutane ne a kasar Japan suka fito domin juyayin harin da aka kai na atomic bomb a Hiroshima da ke kasar Japan, abinda ya hallaka mutane sama da 140,000 a karshen yakin duniya na biyu.

Al'ummar kasar Japan rike da Faranni suna bukin tuna Bala'in Hiroshima
Al'ummar kasar Japan rike da Faranni suna bukin tuna Bala'in Hiroshima Photo AFP / Kazuhiro Nogi
Talla

Wadanda suka tsira da ransu da ‘Yan uwan mamatan da suka mutu da Jami’an tsaro da jekadun kasashen Duniya ne suka kai ziyara Hiroshima.

Da misalin karfe 8:15 agogon kasar Japan ne, Ba’amurke, Enola Gay ya jefa bom a ranar 6 ga watan Agusta shekarar 1945.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a bikin, Angela Kane, ta karanta sakon Ban Ki Moon, tana mai cewa a wannan rana, ba su fatar sake ganin irin wanna lokaci da za’a sake kai harin nukiliya a Hiroshima.

An kiyasta kimanin mutane 5,000 ne suka gudanar bukin, wasu dubun dubatar mutane kuma suka bi zanga-zanga a wajajen ibada da sassan yankunan kasar domin adawa da mallakar makaman Nukiliya a duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.