Masar
Rundunar Sojan Masa ta sha alwashin yin ramuwar gayya, kan sojojinta 16 da aka kashe
Rundunar Sojan kasar Masar a yau litanin ta yi alkawalin daukar Fansar rayukan dakarun tsaron kan iyakarta 16 da yan ta’adda suka kashe a yankin Sinai, kafin su arce a cikin kasar Izraela, bayan da aka kashe 5 daga cikinsu.Wannan hari dai, shine mafi muni da rundunar sojan Masar ta taba gani a mashigin na Sinai, tun bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar da aka yi tsakanin Izraela da Masar a 1979, yarjejeniyar da ta sake maidawa kasar Masar yankin na Sinai ga hannunta.
Wallafawa ranar: