Isa ga babban shafi
Syria

Dakarun Syriya sun bayyana kwace anguwar Salahaddin dake Birnin Alep daga hannun yan tawaye

Dakarun gwamnatin kasar Syriya sun bayyana kama wata anguwa mai muhummanci a garin Alep, bayan wani kazamin harin da suka kai kan yan tawaye, wandanda su kuma suka bayyana cewa, har yanzu sun cikin unguwar ta Salaheddin da suka kama tun ranar 20 ga watan jiya.Majiya Dakarun Gwamnati Bashar Al’assad ta bayyana cewa, an samu hasarar rayuka da dama daga gefen yan tawaye,wani kanal daga bangaren yan tawayen Abdel Jabar Oqeidi ya bayyana cewa, gaskiya ne dakarun gwamnati sun kai kazamin hari a kansu, amma ba gaskiya bane cewa, sun kama daukacin unguwar.A dai gefen kuma rahotannin daga kasar na cewa, an samu karin wasu mutane 2,000 da suka tsere wa yakin da ake yi a kasar, zuwa cikin kasar Turkiyya, cikin su har da manyan Janar na Soja 2.Kafofin samun labarai dake kasar na cewa jimillan ‘yan gudun hijira daga Syria dake kasar Turkiyya yanzu sun haura dubu 50.Bayanan na nuna cewa, Manyan janarori sojan da suka tsere na tafe ne da wasu kananan sojoji da suka kai 35 ciki kuwa akwai masu mukamin kanar su 2. 

wata hanya a anguwar Salaheddin Fayau a tsakkiyar  birnin Alep,  bayan fadan da aka gwabza tsakanin yan tawaye da dakarun Syriya.   8 Ogusta 2012.
wata hanya a anguwar Salaheddin Fayau a tsakkiyar birnin Alep, bayan fadan da aka gwabza tsakanin yan tawaye da dakarun Syriya. 8 Ogusta 2012. REUTERS/Goran Tomasevic
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.