Isa ga babban shafi
Pakistan

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 26 a Pakistan

Ambaliyar ruwa da zaizayan kasa sun hallaka akalla mutane 26 a yayin da daruruwan gidaje su ka salwanta a arewacin kasar Pakistan. Hukumomin kasar sun tabbatar da aukuwan wannan bala’i a yau Alhamis.  

Wani ambaliyar ruwa da ya shafi kasar Pakistan a yankin Siachen.
Wani ambaliyar ruwa da ya shafi kasar Pakistan a yankin Siachen. AFP
Talla

Firaministan kasar, Chaudry Abdul Majeed, ya kara da cewa a ranar Litinin da ta gabata ma mutane 17 ne su ka mutu a gundumomi daban daban a kasar.

A cewar Firaministan, ruwan ya yi awun gaba da hanyoyi da dama, inda ya kuma bayyana cewa tuni an nemi taimakon gwamnatin tarayyara kasar.

Sai dai wani Jami’in hukumar bada agajin gaggawa a kasar, Irshad Bhatti, ya bayyana cewa har yanzu hukumar na nan na kokarin kayyade irin barnar da ambaliyar ruwan ya yi.

Haka kuma, wani jami’i daga yankin Khyber Pakhtunkwa, Adnan Khan, ya ce akwai yiwuwar samun karuwar yawan wadanda su ka jikkata.

Masana yanayi a kasar sun kuma yi hasashen cewa akwai yiwuwar samun wani ruwan sama mai yawa nan da kwanaki uku, a yayin da masu taimakon agaji ke jiran ko ta kwana.

Ambaliyar ruwa a kasar Pakistan, a shekarar 2011, ya shafi mutane miliyan 5.8 inda ambaliyar kan kashe mutane da dabbobin gida, ya kuma shafi amfanin gonaki da gidaje a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.