Isa ga babban shafi
Syria

Dakarun Syria na cigaba da lugudan wuta a Aleppo

Dakarun kasar Syria na cigaba da lugudan wuta a kasar, inda a yau mutane 19 su ka mutu, a cewar wata kungiya mai fafutukar kare hakkin Dan Adam.Wannan ikrarin kungiyar, ya zo ne a dai dai lokacin da sabon wakili na musamma da Majalisar Dinkin Duniya da kasashen larabawa su ka nada, Lakhdar Brahimi ya ce yawan mutanen da su ka mutu abu ne mai girgiza mutun.  

Irin lugudan wutan da ake yi a garin Aleppo
Irin lugudan wutan da ake yi a garin Aleppo Reuters/路透社
Talla

Ya kara da cewa asara kuma da aka tafka na rushe wurare ya zama bala’i.

An dai fara lugudan wutan ne na karshen nan da sanyi safiyar asuba inda mutane 10 su ka fara mutuwa a kudancin garin na Aleppo.

Kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin Dan Adam sun rawaito cewa lugudan wutan da dakarun na Syria ke yi babu kakkautawa, inda su ka kara da cewa, ana kuma fama da matsalar abinci.

Haka kun ‘Yan tawayen na Syria sun kai wani hari akan filin saukan jirgin da ke kira, Albu Kamal a gabashin yankin, Deir Ezzor, da ke kusa da kan iyakar kasar Iraq.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.