Isa ga babban shafi
Lebanon-Isra'ila

Hezbolla tace jirginta ne aka kakkabo a Isra'ila

Shugaban Kungiyar Hezbollah a kasar Lebanon Sayyed Hassan Nasrallah yace mayakan kungiyar ne suka aike da wani jirgin yaki, kirar kasar Iran, wanda aka kakkabo a yankin Isra’ila makon jiya. Jirgin ya yi tafiya mai nisa daga Lebanon kafin a kakkabo shi.

Shugaban Hezbollah Sayyed Hassan Nasrallah
Shugaban Hezbollah Sayyed Hassan Nasrallah REUTERS/Sharif Karim
Talla

Shugaban kungiyar yace jirgin ya ratsa wasu wuraren sirri a kasar Isra’ila, wanda hakan ke nuna shakka babu mallakan wannan jirgi, ya kasance na farko da wata kungiya ta mallaka a Lebanon da yankin Gabas ta tsakiya.

A cewar shugaban ba karo na farko ke nan ba, aka cilla irin wannan jirgi kuma ba zai kasance na karshe ba, kuma jirgin kirar kasar Iran ne , da aka hada a Lebanon.

Ikirarin Jagoran Hezbollah na zuwa ne a dai dai wani lokaci da Firaministan Isra’ila Benjamin Natanyahu ke zargin kungiyar Hezbolla da cilla irin wannan jirgi da aka gaza ganewa, yana mai cewa Isra’ila za ta dauki matakan kare kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.