Pakistan
An dauke Malala zuwa Birtaniya domin kula da lafiyarta
Hukumomin Kasar Pakistan sun dauke Malala Yosoufzai daga Pakistan zuwa Britaniya dan ci gaba da jinya, sakamakon harbin da aka mata a kai, bayan likitoci sun yi nasarar cire harsashin. Rundunar sojin kasar, ta sanar da cewa, an dauki Malala ne dan ganin ta kara samun sauki, tare da bayyana cewa yarinyar bata cikin hadari.
Wallafawa ranar:
Talla
Tuni dai Pakistan ta sanya ladar Dala 100,000 don ganin an gano wadanda suka kai harin, wanda kungiyar Taliban ta dauki alhaki, ta kuma ce zata ci gaba har sai ta hallakata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu