Isa ga babban shafi
Asiya

Kwararru sun yi gargadin yiwuwar bullar zazzabi mara jin magani a Asiya

Kwararru a Nahiyar Asiya sun yi gargadin bullar wani nau’in zazzabin cizon sauro, da baya jin magani. Sun dai yi wannan gargadin ne, yayin babban taron da suka fara yau Laraba a birnin Sydney na kasar Austarlia.  

Taswirar Nahiyar Asiya
Taswirar Nahiyar Asiya www.worldatlas.com
Talla

Darakta mai kula da lafiyar al’ummar, a jami’ar Califaniya, Richard Feachem, ya ce an gano bullar nau’in cutar da bata jin magani a Kasashen Cambodia, Thailand da Myanmar.
 

Ya ce wannan nau’in cutar ta fara bijerewa maganin nan na Artemisinin, da shine kan gaba wajen yakar cutar a halin yanzu, a duk duniya.
 

Feachem, wanda shine tsohon shugaban asusun yaki da cutuka masu yaduwa a duniya, ya ce a baya an fara samun nasara kan cutar, amma akwai yiwuwar wannan bijirewa maganin da take yi, zai bulla kudu maso gabashin Asiya, daga bisani kuma ya iya nausawa zuwa Africa.
 

A halin yanzu, kasashe 22 ne ke fama da Malariya a yankin Asiya da Pacific, sai dai an sami ci gaba matuka wajen yaki da ita, inda cikin shekaru10 da suka wuce yawan masu kamuwa ya ragu da kashi 50 cikin 100.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.