Isa ga babban shafi
Saudiya

Motar Tanka ta yi sandiyar mutuwar mutane 22 a Saudiya

Wata motar Tanka a Saudiyya ta tarwatse a kan wani babban titi dake cikin birnin Makka, inda akalla mutum 22 suka mutu.

Ministan cikin gida na kasar Saudiya, Yarima Nayef
Ministan cikin gida na kasar Saudiya, Yarima Nayef Reuters
Talla

Rahotanni sun bayyana cewar bayaga wadanda suka mutu, wasu 111 sun jikkata ya zuwa wayewar safiyar yau dinnan.

Wakilin Kamfanin Dillancin labarai na kasar faransa AFP, ya bayyana cewar Tankin ya fara yoyo ne, daga bisani kuma ya fashe, abinda yayi sanadin konewar wata Motar Bus dauke da wasu ma’aikatan da ba’a tantance suba ya zuwa yau dinnan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.