Isa ga babban shafi
Falesdinawa-Isra'ila

Faledinawa sun yi zanga-zanga domin adawa da kalaman Abbas

Al’ummar Falesdninawa a Zirin Gaza sun gudanar da wata Zanga zanga domin adawa da kalaman Mahmoud Abbas game da dawowar ‘Yan gudun Hijira daga yankunan da Isra’ila ta mamaye.

Shugaban Faledinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Faledinawa Mahmoud Abbas
Talla

A ranar Jumu’a ne Mahmoud Abbas ya bayyana cewa baya da kudirin karbe ikon arewacin birnin Safed da ke karkashin ikon Isra’ila a yanzu haka.

Kuma kalaman Abbas ya yi wa shugaban Isra’ila Shimon Peres dadi amma kuma dubban al’ummar zirin Gaza ne suka fito suna zanga zanga tare da kona hotunan Mahmoud Abbas.

To sai dai kuma wasu Ministocin Isra’ila suna ganin shugaban Falesdninawan ya fadi haka ne domin raba hankalin Isra’ila a zaben da za’a gudanar a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.