Isa ga babban shafi
Syria

Malamin addini Muaz zai jagoranci ‘Yan tawayen Syria

‘Yan Adawa a Syria sun zabi Moaz al-Khatib tsohon limamin masallacin Umayyad a matsayin wanda zai jagoranci hambarar da Gwamnatin Bashar al-Assad bayan sun gana a Doha babban birnin kasar Qatar.

Sheikh Ahmad Moaz al-Khatib Shugaban Gwamnatin 'Yan tawayen Syria
Sheikh Ahmad Moaz al-Khatib Shugaban Gwamnatin 'Yan tawayen Syria REUTERS/Mohammed Dabbous
Talla

‘Yan adawar sun cim ma wata yarjejeniyar hada kai domin watsi da banbancin Akida, akan haka ne kuma suka zabi Moaz al-Khatib wanda mabiyi akidar Sunni ne.

‘Yan adawar sun dauki wannan matakin ne bayan fuskantar matsin lamba daga Amurka da sauran kasashe domin cim ma yarjejeniyar hada kan juna.

Sheikh Moaz al-Khatib, mai shekaru 52 na haihuwa, a watan Yuli ne ya fice daga Syria zuwa birnin Al Kahira bayan kwashe lokaci mai tsawo yana fuskantar dauri daga mahukuntan Syria.

Rahotanni sun ce sama da mutane 36,000 ne aka kashe tun fara zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bashar al Assad a bara.

 

Daruruwan mutane ne suka yi gudun hijira daga Syria zuwa makwabtan kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.