Isa ga babban shafi
Falestine

Tono gawar Yaseer Arafat bayan mutuwar shi

An Tono gawar Tsohon Shugaban Falesdinawa Yaseer Arafat a yau Talata domin binciken musabbabin ajalinsa. Rahotanni sun ce Masana daga Rasha da Faransa sun dauki Samfurin da za su yi gwaji domin gano ko an yi amfani da Guba ne aka kashe shugaban.

Wata Mata tana tafiya kusa da Hoton Zanen Marigayi tsohon Shugaban Faledinawa Yaseer Arafat wanda za'a tono gawar shi bayan ya Mutu domin gudanar da bincike
Wata Mata tana tafiya kusa da Hoton Zanen Marigayi tsohon Shugaban Faledinawa Yaseer Arafat wanda za'a tono gawar shi bayan ya Mutu domin gudanar da bincike Reuters/Mohammed Salem
Talla

Wata Majiya daga birnin Ramallah ta shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa na AFP cewa da misalin karfe Biyar na safe aka fara binciken Gawar marigayin a gaban Masana daga Rasha da Faransa da kuma Switzerland.

Shekaru Takwas ke nan bayan rasuwan tsohon jagoran Falasdinawa Yaseer Arafat.

Falesdinawa dai suna zargin an kashe shugaban ne da guba, Kamar yadda Matar marigayin, Sunha Arafat ta yi zargin an saka masa Guba ne kamin ya mutu.

Tun a ranar Lahadi ne alkalan Faransa da za su yi aikin gudanar da binciken suka kai ziyara Ramallah inda aka binne shugaban kuma fadar shugaban Falesdinawa Mahmoud Abbas.

A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2004 ne Arafat ya mutu a Asibitin Sojoji a birnin Paris na kasar Faransa, kuma hukumomin Faransa har yanzu ba su ce komi ba game da abinda ya kashe shi inda Falesdinawa ke zargin Isra’ila ce ta yi amfani da guba da ya kashe Shugaban.

Shugaban Falesdinawa Mahmud Abbas ya bayyana fatar ganin binciken ya tabbatar da sahihancin abinda ya kashe shi, sabanin hasashe da ake na cewar ana zaton cutar sankara da cutar kanjamau suka kashe shugaban.

Wannan ne dai karon farko da aka fadi sunan Rasha cikin kasashen da ke binciken gano abin da ya kashe Yaseer Arafat.

Dangin tsohon shugaban suna ganin ko an tono gawar shi babu wani abu da za’a gane amma suna masu ra’ayin kashe shugaban aka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.