Isa ga babban shafi
Palasdinu

Kungiyoyin Hamas da Fatah na shirin hawa teburin sasantawa

Kungiyoyin Falasdinawa masu adawa da juna na Hamas da Fatah sun ce ya yakamata a shimfida sabbin matakan da zasu bada damar kawo karshen rashin jituwan da ke tsakanin bangarorin biyu domin samar da cikakkiyar kasar FalasdinuA wata ziyararsa ta farko a yankin zirin Gaza, shugaban Hamas, Khaled Meshaal, ya ce lokaci ya yi da bangarorin biyu, da basa ga maciji, su hada kansu, su kuma aiwatar da yarjejeniyar da suka rattaba hanu a shekarar 2011.A cewar Meshaal, kasar Falasdinu na da girman da bangare daya bazai iya sarrafata ba, saboda haka Falasdinu tasu ce duka, ya kuma kara da cewa Hamas bazata ta yi tasiri ba tare da Fatah ba, haka itama Fatah baza ta yi tasiri ba tare da Hamas.Shugaban Mahmud Abbas wanda shine shugaban Fatah ya yi maraba da wannan kira da Meshaal ya yi, inda shima ya nemi da a dawo kan teburin sasantawa, yana mai cewa gudanar da zabe shine zai zamanto muhimmin batu.A cewar Azzam al Ahmed, wanda shine mai Magana da yawun Fatah, jawabin na Meshaal nada muhimmanci ta fuskar samar da hukuma daya da doka daya da kuma shugaba daya ga Falasdinawa.A shekarar 2011 ne aka yi yarjejeniyar gudanar da zabe a watan Mayun wannan shekara sai dai takaddama kan wa zai jagoranci gwamnatin wucin gadi ta kawo cikas ga yin hakan.  

Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas yana jawabi a Ramallah
Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas yana jawabi a Ramallah Reuters/Mohamad Torokman
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.