Amurka-Japan
Obama ya zanta da Firaministan Japan mai jiran gado
Shugaban Amurka, Barack Obama ya zanta da Firaminsitan kasar Japan mai jiran gado Shinzo Abe, inda bangarorin biyu suka bayyana bukatar aiki tare don bunkasar tattalin arzikinsu domin adawa da China. Mai Magana da yawun fadar shugaban Amurka ta White House Jay Carney yace shugabannin biyu sun jaddada muhimmancin hade kai tsakaninsu, a matsayin ginshikin tabbatar da zamana lafiya da tsaro.
Wallafawa ranar:
Talla
Jama’iyyar Abe ta LDP ta kayar da Democratic Party ta Yoshihiko Noda, a zaben da aka yi a ranar Lahadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu