Mutane 60 sun mutu a harin Syria
Wani harin sama da sojan gwamnatin kasar Syria suka kai a wani gidan burodi, yayi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 60 tare da raunata wasu 50. Shaidun gani da ido sun ce sun ga gawarwaki warwatse a kan tituna, yayin da aka ga wasu cikin gine-ginen da suka rushe.
Wallafawa ranar:
Harin na yankin Halfaya da ke tsakiyar lardin Hama na zuwa ne a daidai lokacin da mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya, Lakhdar Brahimi, ya fara wani yunkurin kawo karshen rikicin kasar, da ya doshi shekaru 2.
Tawaggar masu sa ido kan rikicin ta ce, wadanda suka sami raunuka sakamakon harin na cikin halin mutu ko-koi-rai-ko-koi, kuma akwai yiwuwar mamatan za su karu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu