Isa ga babban shafi
Iran-Syria

Iran na goyon bayan shugaba Assad kan kin tattaunawa da 'yan tawaye

Yayin da kasashen Yammacin duniya suka fito karara suka yi Allah-wadai da matsayin shugaba Bashar al Assad na kin tattaunawa da ‘Yan tawaye da kuma gabatar da wani shirin zaman lafiya, kasar iran ta bayyana goyan bayanta, da shirin.Ministan harkokin wajen Iran, Ali Akbar Salehi ya bayyana goyan bayan kasar shi kan shirin, inda yake cewa Iran na goyan bayan shirin shugaba Bashar al Assad, na samun dauwamamamen zaman lafiya a cikin kasar.Shirin da shugaban ya gabatar a jawabin daya yiwa yan kasar, ya kunshi watsi da tashin hankali da kuma aiyyukan ta’addanci, da kin amincewa da sanya hannun kasashen ketare a rikicin, inda ya gabatar da shirin siyasa, da yake fatar ganin ya magance halin da ake ciki.Ita dai gwamnatin Iran ta dade tana taimakawa Syria ta wajen tattalin arzikin kasa da kuma shawarwarin soji kan rikicin.Tuni ‘Yan Tawayen Syria da kasashen Yammacin duniya suka yi watsi da bukatar ta shugaba Assad. 

shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinejad.
shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinejad. (Photo : AFP)
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.