Shugaba Hollande na Faransa yana ziyara a kasar India
Shugaban Faransa, Francois Hollande, ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar India, inda ake sa ran zai farfado da cinikin jiragen saman yaki tsakanin kasashen biyu. Wannan ziyarar, ita ce ta farko da Shugaban ya kai Nahiyar Asia, inda Faransa ke fatar ziyarar za ta taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci na shekaru 15, da ke tsakanin kasashen biyu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A cikin tawagar Shugaba Hollande, akwai Ministoci biyar, cikin su har da Ministan harkokin waje Laurent Fabius, da Ministan tsaro Jean Yves Le Drian da kuma 'Yan kasuwa sama da 60.
Ma’aikatar harkokin wajen India tace dangantakar kasashen biyu na ci gaba da karuwa a fannonin kasuwanci, tattalin arziki da kuma masana’antu.
Ana saran shugaba Hollande zai gana da Prime Minista, Manmohan Singh a birnin New Delhi, kafin ya tafi birnin Mumbai don ganawa da ‘yan kasuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu