Isa ga babban shafi
Syria

‘Yan tawayen Syria sun karbe ikon Garin da ke kan iyaka da Iraqi

‘Yan tawayen Syria daga bangaren masu kishin Islama na kungiyar Nusra Front sun karbe ikon birnin Shadadeh yankin Arewa maso gabaci mai arzikin Man Fetir da ke kan iyaka da kasar Iraqi.Wannan kuma na zuwa ne bayan ‘Yan tawaye sun kakkabo wani jirgin yakin Syria a yankin Arewa maso yammacin Idlib.

Marat al-Numan, Arewacin yankin  Idlib
Marat al-Numan, Arewacin yankin Idlib REUTERS
Talla

‘Yan rajin kare hakkin Bil’adama da ke sa ido a rikicin Syria sun ce an kwashe tsawon kwanaki uku ‘Yan tawayen suna musayar wuta da dakarun Gwamnatin Syria.

Akalla mutane 100 aka ruwaito sun Mutu a hare haren Bama bamai da ‘Yan tawayen suka kai a yankin Hasake.

Rahoranni kuma sun ce ma’aikata da dama ne suka mutu da ke aiki a kamfanin Mai a garin Shadadeh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.