Isa ga babban shafi
Syria

An kashe mutane 49 cikinsu har da babban malamin addinin musulunci a Syria

Akalla mutane 49 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu cikinsu kuwa wani babban malamin addinin musulunci mai goyon bayan shugaba Basharul Assad a cikin wani masallaci da ke birnin Damaskus a yammacin jiya alhamis.

Reuters/Hamid Khatib
Talla

Kamfanin dillancin labaran kasar Syria wato SANA, ya tabbatar da cewa harin an kai shi ne a masallacin Al-iman da ke unguwar Mazra’a a birnin na Damaskus, kuma harin ya yi sanadiyyar mutuwar wani babban limamin ‘yan Sunnah da ke goyon bayan Assad mai suna Mohammad Said Al-Bouti.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta Syria ta fitar a safiyar yau juma’a ta bayyana harin da cewa wani aiki ne na marasa hankali wadanda kuma ba su damu da makomar kasar ta Syria ba.
Jagoran ‘yan adawa a kasar ta Syria Ahmed Moaz Al-khatib ya yi kakkausar suka a game da wannan hari wanda aka kai ta hayar fasa bam a cikin masallacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.