Isa ga babban shafi
Pakistan

Wani dan siayasan Pakistan ya mutu sakamakon musayar wuta

RAHOTANNI daga Pakistan na nuna cewa wata musayar wuta da aka tsakanin jami’an tsaro da masu kula da lafiyar wani dan takara a zaben da za a gudanar a kasar, ya yi sandiyar mutuwar dan takarar.Abdul Fateh, wanda dantakarar kujerar majalisar ne, ya rasa ransa ne bayan musayar wutar da ta biyo bayan kin tsayawan da motar shi ta yi, a wani shinge bincike a yankin Baluchistan.A cewar Sakataren yankin, Akbar Hussain, jami’an tsaron da aka ajiye a shigen binciken, sun nemi motar dake dauke da dan siyasan ta tsaya, amma hakan ya cutura, lamarin da sa suka bude wuta kan matar, kuma dan takarar tare da masu tsaren lafiyarsa su biyu, a cewar Sakataren suka rasa rayukansu.Binciken da aka gudanar a cikin motar dan siyasar, ya sa an gano manyan makamai, wanda hakan ya sa aka kama sauran mutane biyar dake jerin gwanon motar dan siyasan.Yankin Baluchistan na kasar ta Pakistan ya kasance daya daga cikin yankunan da ake yawan samun tashe tashen hankula a ‘yan kwanan nan musamman saboda wannan guguwar siyasar.Tuni dai kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta yi kira ga hukumomin kasar da su hanzarta binciki lamarin tashe tashen hankula a yankin. 

alamar zaben kasar Pakistan
alamar zaben kasar Pakistan Brooke Slezak/Klenger/Terrade
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.