Isa ga babban shafi
kasashen Larabawa

Amurka na fatan ganin an hana yaduwar Nukiliya a Gabas ta tsakiya

Amurka na ci gaba da fatan taron da ake shirin yi, kan samar da yarjejeniyar hana amfani da makaman Nukiliya a yankin gabas ta tsakiya, ya kankama cikin hanzari. Mataimakin sakatern da ke kula da tsaro a kasashen waje, da hana yaduwar makama Nukiliya, Thomas Countryman, yace za a iya gudanar da taron cikin hamnzari, in har masu ruwa da tsaki a yankin na gabas ta tsakiya suna fatan samun nasara shi.Countryman, da ke magana a birnin Geneva, ya ce kasashen Amurka, Britaniya, Rasha da ma Majalisar Dinkin Duniya, da suka kuduri amiyar shirya taron a birnin Helsinki din kasar Finland a baya, suna fatan ganin an sami nasara a kai.A watan mayun shekarar 2010, aka yi kira don gudanar da taron, da zai sake duba yarjejeniyar shekarar 1970, da ke hana yaduwar makaman na nukiliya, amma ba a samu damar gudanar da shi, a shekarar da ta gabata, kamar yadda aka tsara ba, saboda adawa daga kasar Isra’ila, da ta ki halarta, saboda zaman dar dar da ake yi a yankin, da kuma fargabar shan suka daga mahalarta. 

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama . REUTERS/Yuri Gripas
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.