Isa ga babban shafi
Afghanistan

Wani mutum ya kashe 'Yar shi a Afghanistan

Wani Mutum ya zartar da hukuncin kisa ga ‘Yarsa, a kan zargin aikata zina, a kasar Afghanistan. Mutumin ya ya bindige diyar tashi mai suna Halima har lahira a gaban daruruwan mutane, lamarin da ya bayyana da janyo abin kunya ga iyalan nasu, bayan da mutanen kauyen nasu suka fara zolayar shi, kan lamarin.Halima ‘yar shekaru tsakanin 18 zuwa 20, mai ‘yaya biyu, ta tsre ne tare da wani dan uwan ta, bayan da mijin ta ya tafi kasar Iran. ‘Yan sandan Afghnaistan sun ce mahaifin ya dauki matakin yanke mata hukunci ne bayan da aka kama Halima, inda ya nemi shawara daga malaman da ke da goyon bayan ‘yan kungiyar Taliba, kan yadda zai hukunta ta.Sau da dama ‘ya ‘ya mata suna fuskantar tsauraran matakai, daga wajen iyaye da dangin su, in aka zarge su da aikata zina. Sau da dama ana zartar da irin wannan hukuncin a kasar ta Afghanistan, ba tare da bin ka’idojin shari’a ba.Sai dai ‘yan sandan sun ce har yanzu ba wanda aka kama sakamakon kisan. 

Wasu matan kasar Afghanistan
Wasu matan kasar Afghanistan
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.