Isa ga babban shafi
Pakistan

‘Yan adawa sun kauracewa zaben shugaban kasa a Pakistan

Babbar jam’iyyar adawa a kasar Pakistan PPP, ta ce ba za ta shiga zaben da za a gudanar a ranar 30 ga wannan watan ba, kamar yadda Kotun Kolin kasar ta bukaci a yi, tana mai bayyana cewar an gurguso da zaben sabanin yanda ya kamata ya kasance.

Hotunan 'yan takara a Pakistan
Hotunan 'yan takara a Pakistan REUTERS/Damir Sagolj
Talla

Jam’yyar ta ce za ta kauracewa zaben ne domin kuwa an tsayar da ranar gudanar da shi ne ba tare da an tuntube ta. Yanzu haka dai akwai ‘yan takara ashirin da hudu da ke neman mukamin, kuma Majalisar Dokokin kasar ce ke zaben shugaban kasa.

‘Yan Majalisu da dama sun kalubalanci Jma’a da su tabbatar da ganin cewar sun zabi wani mutum da zai gaji shugaba Asif Ali Zardari, inda suka bayyana cewar zasu gudanar da Addu’o’I a karshen Watan Ramadana.

An dai bayyana cewar akalla ‘yan takara 24 ne zasu kar da juna a takarar neman Kujerar shugabancin kasar.

Babban jami’in bangaren ‘yan adawa ya bayyana cewar basu da wani zabin da ya wuce su kauracewa wanan zaben.

Dama dai ‘yan Majalisun Dokoki dana Wakilai ne zasu gudanar da zaben sabon shugaban da kuma manyan wakilai daga sassan ‘yan majalisu Hudu dake a kasar ta Pakistan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.