Isa ga babban shafi
Pakistan

Taliban ta kubutar da mayakanta a gidan yarin Pakistan

Fursunoni akalla 243 ne cikinsu kuwa har da ‘Yan ta’adda aka tabbatar da cewa sun tsere daga wani gidan yarin kasar Pakistan lokacin da wasu mahara suka afkawa gidan yarin ta hanyar yin harbi da bindigogi da kuma jefa abubuwa masu fashewa a kan jami’an tsaro.

Gidan yarin Dera Ismail, da kungiyar Taliban ta kai hari a Pakistan
Gidan yarin Dera Ismail, da kungiyar Taliban ta kai hari a Pakistan AFP PHOTO / STR
Talla

Mustaq Jadoon wani jami’in gwamnatin kasar ya ce tuni suka cafke shida daga cikin fursunonin, yayin da ya ce maharan sun kashe mutane 12 cikinsu har da ‘yan sanda hudu.

‘Yan bindigan sun kai harin ne a babban gidan yarin da ake ajiye ‘Yan ta’adda a garin Dera Isma’il Khan, da ke yankin Khyber Pakhtunkhwa

Wata majiyar Soji tace gidan yarin yana dauke ne da ‘Yan gidan yari 5,000 cikinsu kuma kawai ‘Yan ta’adda 300 wadanda suka kai wa Jami’an tsaro hari.

Tuni kuma kungiyar Taliban ta fito ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin a gidan yarin.

Kakakin kungiyar Shahidullah Shahid ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa mayakansu kimanin 150 ne suka kai harin domin kubutar da ‘Yan gidan yarin.

Jami’an tsaron Pakistan sun ce an kwashe tsawon sa’o’I uku ana musayar wuta tsakaninsu da Mayakan wadanda suka yi shigar ‘Yan sanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.