Isa ga babban shafi
Syria-Turkiya

An yi garkuwa da Kurdawa a kan iyakar Syria da Turkiya

Masu dauke da makamai da ake dangantawa da kungiyar Al Qaeda sun yin garkuwa da mutane akalla 200 dukkaninsu kurdawa a wasu yankuna da ke kusa da iyaka tsakanin Syria da Turkiya. Wata kungiya mai zaman kanta da ke yankin ce ta tabbatar da hakan.

Kurdawan Syria suna zanga-zanga a Wamishli a ranar Juma'a bayan kammala Sallah
Kurdawan Syria suna zanga-zanga a Wamishli a ranar Juma'a bayan kammala Sallah Reuters
Talla

Kungiyar ta ce mayakan kungiyar Al-Nosra da kuma wata kungiyar mai cewa tana fatar kafa kasar musulunci a cikin Iraki, wadanda suka shiga Syria domin fada da gwamnatin Bashar Assad, su ne ke yin garkuwa da fararen hular.

A daya bangare kuma mai Magana da yawun babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Martin Nersiky, ya ce nan ba da jimawa ba ne jami’an Majalisar za su isa kasar ta Syria domin gudanar da binciken kan makamai masu guba bayan da gwamnatin Assad ta amince da hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.