Isra’ila za ta saki Falesdinawa 26 'Yan Gidan Yari
Gwamnatin Isra’ila ta ce za ta saki Karin wasu Falastinawa 26 wadanda suka fi dadewa tsare a gidajen yarinta, wannan kuwa domin sauwaka tattaunawar sulhun da za a ci gaba da yi tsakanin bangarorin biyu a jibi Laraba.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwa da hukumomin kasar suka fitar, ta bayyana cewa wadanda za a saka, suna daga cikin jerin fursunoni 104 dukkaninsu Falsdinawa da kuma Larabawan Isra’ila wadanda aka cafke tun kafin kulla yarjejeniyar Oslo ta shekarar 1993.
A gobe Talata ne ake sa ran sakin Falesdinawan, kuma wannan sanarwar na zuwa ne bayan shugabannin Falesdinawa sun zargi Isra’ila da kokarin yin zagon kasa ga yunkurin samun sulhu bayan Isra’ila ta fitar da sanarwar ci gaba da gina wasu sabbin matsugunin Yahudawa a yankunan da ta mamaye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu