Myanmar
Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a sulhu a rikicin kasar Myanmar
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci hukumomin kasar Myanmar da su buda tattaunawa domin shawo kan sabanin da ake fama da shi tsakanin musulmi da kuma mabiyar addinin Buddha na kasar, wadanda sakamakon rikicin da suke yi da junansu aka samu asarar rayukan mutane da dama a cikin shekarar bana.
Wallafawa ranar:
Talla
Kiran na MDD dai ya zo ne bayan da wasu rahotanni ke cewa an samu barkewar tashin hankali tsakanin musulmi ‘yan kabilar Rohingya da kuma ‘yan Buddha, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum daya da kuma raunata wasu 10.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu