Isa ga babban shafi
Pakistan-Afghanistan

Karzai ya nemi hadin kan Pakistan don sasantawa da Taliban

Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai ya nemi kasar Pakistan ta samar da hanyoyin tattaunawa da kungiyar Taliban tare da kiran hadin kan kasashen biyu domin ya ki a lokacin da shugaban ke ziyarar aiki a Islamabad domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a tsakanin kasashen biyu.

Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai yana ganawa da Firaministan Pakistan Nawaz Sharif
Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai yana ganawa da Firaministan Pakistan Nawaz Sharif REUTERS/Mian Khursheed
Talla

Wannan ita ce ziyara ta farko da shugaba Karzai ke gudanarwa a kasar a cikin watanni 18, a dai dai lokacin da dakarun Kungiyar Tsaro ta NATO karkashin jagorancin Amurka da yawansu ya kai dubu 87 ke shirin ficewa daga kasar a shekara mai zuwa.

A baya, Afghanistan ta nuna rashin amincewa da kudirin bude ofishin sasantawa da Taliban a kasar Qatar da Amurka ke jagoranta, amma Karzai yanzu ya bukaci hadin kan kasar Pakistan.

Amma akwai gargadi da Taliban ta yi na yin watsi da duk wani kudirin tattaunawa da Karzai wanda suka kira dan koren Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.