Isa ga babban shafi
Syria

Siriya tace ko da Yakin Duniya na Ukku zai barke ba zata bada Kai ga Amurka ba.

Kasar Siriya ta bayyana cewar ba zata bada Kai Bori ya hau kan barazanar kai harin da Amurka ke mata ba, ko da yakin Duniya na Ukku ne zai barke. Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kasashen yammacin Duniya ke ci gaba da neman hanyoyin da zasu afkawa kasar.

Talla

Ministan harkokin wajen kasar ta Siriya Faisal Maqdad ne ya bayyana cewar gwamnatin Siriya dai ta kimtsa domin kare kanta daga harin Amurka, harma yana bayyana cewar ko da Yakin Duniya na 3 ne zai barke, to ba zasu jaa da baya ba.

Yanzu haka dai ‘yan Majalisar kasar Faransa na can suna tafka muhawara akan kudurin shugaba Hollande na marawa Obama kai hari a Siriya

Ko a ziyarar da ya kai yau dinnan a Stockholm shugaban kasar Amurka barack Obama, ya bayyana cewar gwamnatocin kasa-da-kasa ba zasu yi shiru akan matsalar ta kasar Siriya ba, bisa zargin da ake yiwa shugaba Bashar al-Assad na amfani da Makami mai Guba.

Obama yace shi da Piraiministan kasar Sweeden sun tattauna akan wannan batu, kuma ba zasu yi shiru akan wannan al’amari ba.

‘yan Majalisar kasar Amurka dai sun bata tsawon Yinin Jiya suna tafka muhawarar amincewa ko rashin amincewa da wannan bukata ta Obama.

A karon farko dai akasarin ‘yan Majalisar sun nuna kin amincewa da wannan bukata na Obama, amma daga bisani bayan da wasu muhimman mutane da suka hada da shugaban Majalisa da ya bayyana cewar wannan batun abu ne da kasar Amurka a matsayinta na kasa ke bukatar yi.

Yace shi yana goyon bayan matakin da shugaba Obama ya dauka ya kuma yi amannar cewar ‘yan majalisar zasu goyi bayan hakan.

Shugaba Barack Obama daya tsaya kyam akan cewar batun kai hari a kasar Siriya kam babu makawa, yace babban abinda zan kara yiwa Amurkawa bayani akai anan shi ne wannan ba Iraqi b ace ba kuma Afghanistan b ace, wannan Hari ne na dan takaitaccen lokaci da zai aika sako ba ga gwamnatin shugaba Assad kurum ba, harma da wasu Kasashe dake da ra’ayin gwada yin kememe ga wannan Doka ta kasa da kasa cewar akwai hukuncin daya rataya a kan su.

A da dai kasar Rasha mai marawa Siriya baya, ta fara jibge manyan kayan fada masu Samfurin S-300 da kuma ke daga cikin hatsabiban Makamai da ake dasu a Duniya a kasar Sirya da manufar taimakawa shugaba Bahar al-Assad, amma kuma bayannan dake fitowa yanzu haka na nuna cewar Rasha ta dakatar da kai Makaman duk da cewar tuni wasu sun isa hannun kasar ta siriya.

Piraiministan kasar Burtaniya David Cameroun wanda ya kasa samun amincewar Majalisar kasar domin kai farmaki a Siriya, ya yi gargadin cewar muddin Amurka ta rafashe, to akwai yiyuwar Assad ya kara amfani da Gubar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.