Iran-Amurka
Iran bata da shirin gina makamin nukiliya
Shugaban Kasar Iran, Hassan Rouhani yace kasar sa bata da shirin gina makamin nukiliya, yayin da ya yaba da wasikar da shugaba Barack obama ya rubuta masa.
Wallafawa ranar:
Talla
A hirar da yayi da wata tashar talabijin na Amurka, Rouhani ya ce yana da damar tattaunawa da kasashen Yammacin duniya kan shirin kasar na samun makamashin nukiliya.
Shugaban ya kuma bayyana aniyar sa na zuwa Amurka makon gobe, dan halartar taron Majalisar Dinkin Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu