Isa ga babban shafi
Iraqi

Akalla mutane 57 ne suka mutu a harin da aka kaiwa masu jana’iza yau a Iraqi

Wani tashin Tagwayen Boma-Bomai guda biyu da aka kaiwa masu zaman makoki a yankin ‘yan Shi’a a kasar Iraqi sun hallaka akalla mutane 57. Bomaboman dai sun tashi ne kusa da wani Kabarin da aka kai wani daya mutu a birnin Sadar na Arewacin Baghdada.  

Harin Iraqi
Harin Iraqi dawn.com
Talla

Harin Boma boman dai ya auku ne a dai dai lokacin da wasu masu Jana’iza ke kokarin binne wani mamaci birnin Sadr.

Baya ga wadanda suka mutu dai akwai wasu jami’an tsaro 10 da aka bayyana cewar na cikin jerin wadanda suka rasa Rayukan su.

Ana dai zargin hukumomi a kasar ta Iraqi da kasa magance yawan tashe-tashen hankulla dake ci gaba da wanzuwa a kasar ta Iraqi tun cikin shekarar 2008.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.