Fransa ba zata yarda kasar Iran ta mallaki makamin Nukliya ba
Shugaban Faransa wanda ke gabatar da jawabi a gaban Majalisar dokokin Isra’ila a yammacin jiya, ya ce Faransa ba za ta amince da cire wa kasar Iran takunkuman karya tattalin arziki da aka kakaba ma ta ba, sai zuwa lokacin da kasar ta dakatar da shirinta na nukilya.
Wallafawa ranar:
Jawabin shugaban kasar ta Faransa dai, ya mayar da hankali ne kan batutuwa da dama da suka hada da batun nukiliyar kasar ta Iran, inda yake cewa, Faransa na nan akan bakantata, kuma ba za ta taba ja da baya dangane da wannan matsayi nata ba.
Hollande ya ce, Faransa ba za ta bar Iran ta mallaki fasahar kera makamin nukiliya ba, kuma ta hanyar tsaurara takunkuman da ke kan kasar ne, za a iya hanata samun irin wannan makamin.
A wani bangare na jawabin nasa kuwa, Francois Hollande ya ce akwai bukatar Isra’ila da kuma Palastinu su ci gaba da tattaunawa domin warware batun gina matsugunan Yahudawa, wanda ke neman yi wa shirin zaman lafiya a tsakaninsu kafar angulu.
To sai dai Hollande ya ce, yana goyon bayan ganin birnin Quds ko kuma Jerusalem, ya ci gaba da kasancewa fadar gwamnatocin Isra’ila da kuma Palastinu, wanda a’l’ummomin biyu za su rayu cikin kwancinyar hankali a tsakaninsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu