Isa ga babban shafi
Yemen

An samu sulhu tsakanin Mayakan Shi’a da ‘Yan kabilar Hashid a Yemen

Mayakan Shi’a a kasar Yemen da ‘yan bindiga na kabilar Hashid da ke arewacin kasar sun amince da su tsagaita wuta, bayan an kwashe kwanaki uku ana fatawa. Majiyoyi daga yankin sun gaskata wannan yarjejeniya.

Jami'an tsaron kasar Yemen a Sanaa babbar birnin kasar
Jami'an tsaron kasar Yemen a Sanaa babbar birnin kasar REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

A ranar Litinin ne wasu ‘Yan tawayen Shi’a suka nemi kwace garin Wadi Khaywan da Usaimat, mazaunin ‘Yan kabilar Hashid da ke lardin Amran.

An samu lafawar rikicin ne bayan da gwamnatin kasar Yemen ta shiga tsakani inda bangarorin biyu suka amince da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Bangarorin biyu kuma sun amince a samar da jami’an da zasu kula wajen tabbatar da ci gaban yarjejeniyar tare da amincewa su fice yankunan da suka mamaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.