Isa ga babban shafi
Korea

Koriya ta Arewa da ta Kudu za su gudanar da taron hadin gwiwa

Yau laraba Kasashen Koriya ta Kudu da ta Arewa, sun amince da gudanar da taron hadin guiwa tsakanin iyalan da yaki ya raba a kasashen 2, yinkurin da ya kasance na farko a cikin shekaru 3 da suka gabata.An bayyana cimma wannan yarjejeniyar ne bayan wata ganawa da manyan jami’an kasashen 2 suka yi, a wani gari mai suna Panmunjom dake kan iyakokin kasashen, inda a 1953 suka sanya hannu kan yarjejeniyar da ta kawo karshen yaki a tsakaninsu.Ana sa ran kasashen 2 zasu gudanar da wani zaman taro a ranakun 20 zuwa 25 ga wannan wata da muke ciki, a garin Kumgang dake cikin kasar Koriya ta arewa, inda kasashen suka saba gudanar da wasu taruruka kamar yadda ofishin ministan sake fasalta kasar Koriya ta kudu ya sanar.A baya dai kasashen na koriya sun sha jarabta kokarin cimma matsaya kan gudanar da taron tsakanin iyalan bangarorin 2, amma abin yaci tura. Tattaunawar da aka yi tsakanin kasar Koriya ta Arewa da kuma kungiyar bayar da agaji ta Red Cros ta kasar koriya ta Kudu a watan Agustan bara ta cimma nasarar kulla yarjejeniyar a tsakaninsu.Za a iya cewa dai duk wata yarjejeniyar da za a iya cimmawa tsakanin makiya 2 abin so ce, matsawar mahukumtan Pyongyang da na Seoul da suka share tsawon shekaru suna ta kokarin ganin sun samu nasarar cimma yarjejeniya kan mafi kantakntar abin da zai hadasu, sun bada hadin kai wajen magance rishin jituwar dake tsakaninsu. 

Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un
Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un Reuters/路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.